Isa ga babban shafi

Jam'iyyun adawar Afrika ta Kudu 17 sun hade kai don kalubalantar Ramaphosa

Bayan gudanar da taron tsawon kwanaki biyu da ya biyo bayan shafe watanni suna tattaunawa, jam’iyyun adawa 7 a Afirka ta Kudu sun kulla yarjejeniyar hadin-gwiwar tunkarar zabukan kasar da ke tafe a shekarar 2024 da nufin hada karfi wajen kawo karshen jagorancin jam’iyya mai mulki ta ANC da shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ke jagoranta. 

Shugaba Cyril Ramaphosa na Afrika ta kudu.
Shugaba Cyril Ramaphosa na Afrika ta kudu. AP - Ramil Sitdikov
Talla

Gamayyar ‘yan adawar sun kuma bukaci sauran jam’iyyun da ba su shiga cikin yarjejeniyar tasu ba da su gaggauta garzayowa domin bayar da tasu gudunmawar wajen kawo karshen mulkin ANC a Afirka ta Kudu, wadda suka ce ta gaza wajen sauke nauyin da ke kanta na jagoranci na gari. 

Wannan dai shi ne karo na farko tun shekarar 1994, da jam’iyyar African National Congress mai mulkin Afirka ta Kudu ke fuskantar barazanar rasa rinjayen da take da shi a zauren majalisar dokokin kasar a zaben shekara mai zuwa, kayen da zai kai ta ga rasa kujerar shugabancin kasar baki daya. 

Tsaka mai wuyar da jam’iyyar ANC ta fada ya biyo bayan zargin gwamnatinta da gazawa wajen magance matsalar cin hanci da rashawa, da  rashin wadatar wutar lantarki da kuma koma-bayan tattalin arzikin kasa, musamman ta fuskar karuwar marasa ayyukan yi.  

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.