Isa ga babban shafi

Afrika ta Kudu ta yi amai ta lashe kan ficewa daga kotun duniya

Fadar gwamnatin Afrika ta Kudu ta ce kasar ba ta da niyyar ficewa daga karkashin kotun duniya ICC, kamar yadda shugaba Cyril Ramaphosa ya bayyana a ranar Talata, abinda ta danganta da kuskuren musayar bayanan da aka samu daga jam’iyya mai mulki wato ANC.

Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa.
Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa. AP - Themba Hadebe
Talla

Sa’o’i kafin wannan sanarwar dai shugaban Ramaphosa ya bayyana cewa jam'iyyar ANC mai mulkin Afirka ta Kudu ta bukaci kasar da ta fice daga karkashin kotun hukunta manyan laifuka ta duniya, wadda a watan Maris ta bayar da sammacin a kamo mata shugaban Rasha  Vladimir Putin, da take zargi da aikata laifukan yaki a Ukraine.

Gabanin kiran na ANC dai Afirka ta Kudu ta dade tana shan suka daga kasashen yammacin Turai, tun bayan barkewar yakin Ukraine saboda kusancinta da Rasha.

A  halin da ake ciki kuma kasar ce dai za ta karbi bakuncin taron kolin kungiyar BRICS wadda ta kunshi  Afirka ta Kudun, da Brazil, da China, da India, da kuma Rasha a watan Agusta.

A matsayinta na mamba na kotun ICC kuma, kamata yayi gwamnatin kasar ta kama shugaban na Rasha idan ya shiga cikinta.

Sai dai a yayin da yake karin bayani kan matsayin jam’iyyarsa ta ANC, shugaba Cyril Ramaphosa ya ce shirin ficewarsu daga kotun ICC ya zarce batun kama Putin, za su yi hakan ne saboda yadda kotun duniyar ba ta yi wa wasu kasashe adalci.

Amma sa’o’i bayan sanarwar fadar gwamnati ta ce an samu kuskuren musayar bayanan da ya kamata a sanar, domin an tattauna batun yiwuwar ficewa daga kotun ta ICC ne a taron kolin jam'iyyar ANC, amma ba shawarar aka yanke ba.

Idan za a iya tunawa dai ko a shekarar 2016 sai da kasar  ta so ficewa daga kotun duniyar, amma kotun kolinta ta dakile yunkurin.

A waccan lokacin dai Afirka ta Kudun ta ki aiwatar da  umarnin kotun duniyar ta ICC ce dangane da sammacin kama tsohon shugaban Sudan Omar Al Bashir, duk da cewar ya kai ziyara birnin Pretoria.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.