Isa ga babban shafi
ICC

ICC ta samu Afrika ta kudu da laifin kin kame Al Bashir

Kotun duniya da ke hukunta laifufukan yaki ta ce kasar Afirka ta Kudu ta saba wa dokokin kasa da kasa, saboda kin kama shugaban Sudan Umar Al-bashir lokacin da ya ziyarci kasar a shekarar 2015 duk da cewa kasar na da masaniya dangane da sammacin kama shi da kotun ta fitar.

Fatou Bensouda babbar mai gabatar da kara a kotun ICC da Shugaban Sudan Omar Al-Bashir
Fatou Bensouda babbar mai gabatar da kara a kotun ICC da Shugaban Sudan Omar Al-Bashir AFP/Isaac Kasamani/Khaled Desouki/Montage RFI
Talla

Kotun ta bayyana matakin kin kama shugaba Al-bashir, a matsayin babban da Afirka Afrika ta kudu ta aikata a matsayinta mamba cikin kasashen da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar da ta kafa kotun.

A watan Yunin 2015 ne Al Bashir ya halarci taron Tarayyar Afrika da aka gudanar a Johannesburg amma kuma shugaban ya fice salin-alin duk da tuntubar juna tsakanin kotun ICC da hukumomin Afrika ta kudu.

Kotun ta ce Afrika ta kudu ta hana ta hukunta Al Bashir kan laifukan yaki 10 da ta ke tuhumarsa da aikatawa a yankin Darfur.

Sau biyu Kotun ICC ke fitar da sammacin kamo Al Bashir, a 2009 da 2010 amma har yanzu yana kan madafan iko a Sudan.

Afrika ta kudu ta ce ta ki kama Al Bashir ne saboda tana ganin ya dace yana da kariya a matsayin shi na shugaban kasa.

Kasashen Afrika dai sun jima suna sukar kotun ICC da aka kafa a 2002 wacce suke ganin ta koma tamkar Karen farautar kasashen yammaci akan shugabannin Afrika.

Duk da ‘Yar Afrika ce shugabar kotun Fatu Bensouda amma shugabannin na ganin kotun ta fi mayar da hankalinta akan su sabanin wasu shugabannin duniya da suka aikata laifukan yaki musamman ta’asar da aka yi a Iraqi zamanin yaki da Saddam Hussian.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.