Isa ga babban shafi

Jam'iyya mai mulki a Afirka ta Kudu na son kasar ta fice daga kotun ICC

Shugaba Cyril Ramaphosa ya ce jam'iyyarsa ta ANC mai mulki ta yanke shawarar cewa ya kamata Afirka ta Kudu ta fice daga kotun hukunta manyan laifuka ta duniya, wadda a watan da ya gabata ta bayar da sammacin kama shugaban Rasha Vladimir Putin.

Shugaban Afirka ta Kudu kenan, Cyril Ramaphosa
Shugaban Afirka ta Kudu kenan, Cyril Ramaphosa AP
Talla

Kotun ta ICC ta bayar da sammacin kama Putin a watan Maris wanda ke nufin gwamnatin Pretoria, wadda za ta karbi bakuncin taron kungiyar BRICS da ta kunshi kasashen Brazil, Rasha, Indiya, China da Afirka ta Kudu a wannan shekara, dole ne kasar ta tsare shi idan ya isa.

Ramaphosa ya ce matakin da ya biyo bayan taron da jam'iyyar ANC ta gudanar a karshen mako, an cimma matsaya ne saboda abin da ake ganin na rashin adalcin da kotu ke yi wa wasu kasashe.

Sammacin kama Putin ya biyo bayan zargin da ake yiwa fadar Kremlin na diban kananan yara daga Ukraine ba bisa ka'ida ba.

Afirka ta Kudu na da alaka ta kut-da-kut da Rasha tun shekaru da dama zuwa lokacin da fadar Kremlin ta goyi bayan yakin da ANC ke yi da wariyar launin fata.

Kasar dai ta ki yin Allah wadai da mamayar da aka yi wa Ukraine wanda ya mayar da birnin Moscow saniyar ware a fagen kasa da kasa, tana mai cewa za ta ci gaba da kasancewa a tsakiya, inda ta gwammace zaman tattaunawa don kawo karshen yakin.

Wannan dai ba shi ne karon farko da Afirka ta Kudu ke yunkurin ficewa daga kotun ta ICC ba.

Kassar ta yi yunkurin ficewa a shekarar 2016 bayan takaddamar da ta barke, lokacin da shugaban kasar Sudan na wancan lokaci Omar al-Bashir ya ziyarci kasar domin halartar taron kungiyar Tarayyar Afirka.

Afirka ta Kudu ta ki kama shi, duk da cewa shugaban na wancan lokacin yana fuskantar sammacin kama shi a kotun ICC kan zargin aikata laifukan yaki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.