Isa ga babban shafi

Isra'ila ta dawo da kai sabbin hare-hare sassan yankin Gaza

An kawo karshen yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Hamas da Isra’ila ba tare da sanarwar tsawaita ko kuma yarjejeniyar ta dindindin ba, kuma tuni Isra’ila ta ci gaba da kai hare-hare yankin Gaza ta kasa, dai dai lokacin da sakataren wajen Amurka Anthony Blinken da ke ziyara a Tel Aviv ke cewa akwai bukatar Isra’ilan ta baiwa fararen hula kariya yayin hare-harenta a yankin na Falasdinu.

Yankin da Isra'ila ta kai hare-hare Gaza da sanyin safiyar yau Juma'a bayan karewar yarjejeniyar tsagaita wuta.
Yankin da Isra'ila ta kai hare-hare Gaza da sanyin safiyar yau Juma'a bayan karewar yarjejeniyar tsagaita wuta. AFP - MOHAMMED ABED
Talla

Da sanyin safiyar yau Juma’a Sojin Isra’ila sun yi luguden wuta a yankunan Rafah da kudancin Gaza inda zuwa yanzu ma’aikatar lafiyar yankin na Falasdinu ke cewa an kashe mutanen da yawansu ya kai 21 baya ga jikkata wasu masu tarin yawa galibi mata da kanaan yara.

Wannan hare-hare na Isra’ila na zuwa ne a dai dai lokacin da saataren harkokin wajen Amurka Anthony Blinken ke kamala ziyarar shi a Tel Aviv inda jirginsa ya tashi a safiyar yau kuma ake saran ya yada zango a hadaddiyar daular larabawa.

Mintuna kalilan gabanin kawo karshen yarjejeniyar tsagaita wutar da misalin karfe 7 na safe ne al’ummar Gaza suka sanar da jiyo karar harbe-harbe ta tashin bama bayan da tun farko Isra’ila ta girke dakaru na musamman da ke zaman jiran lokaci don ci gaba da kashe-kashe a yankin.

 Yankunan da hare-haren na Isra’ila suka shafa sun kunshi Arewacin zirin Gaza da yankin Maghazi na tsakar Gaza kana kudancin da kuma Khan Younis da kuma Rafah.

Zuwa yanzu Isra'ila ta rushe kashi 60 na gine-ginen da ke yankin na Zirin Gaza.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.