Isa ga babban shafi

Hamas da Isra'ila sun sake tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta

Isra’ila da Hamas sun amince da kara tsawaita yarjejeniyar da ke tsakaninsu da akalla kwana guda, matakin da ke zuwa mintuna kalilan gabanin kawo karshen makamanciyar yarjejeniyar ta kwanaki 6 da aka faro.

Mayakan Hamas yayin mika fursunonin Isra'ila da ke hannunsu.
Mayakan Hamas yayin mika fursunonin Isra'ila da ke hannunsu. © AFP
Talla

Wannan mataki dai zuwa ne bayan tsanantar kiraye-kirayen ganin an dauki wannan mataki, inda sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ke mika bukatar ganin an samar da yarjejeniyar dindindn tsakanin bangarorin biyu tare da isar da kayakin agaji cikin gaggawa a Gaza.

Sai dai sanarwar ma’aikatar tsaron Isra’ila ta ce an dauki matakin kara kwana guda a yarjejeniyar ne, don samun damar sakin karin fursunonin Isra’ila da ke tsare a hannun kungiyar Hamas.

Da misalin karfe 6 na sanyin safiyar yau ne yarjejeniyar farkon ke shirin kawo karshe sai dai an dauki matakin bayan sakin Falasdinawa 30 a daren jiya Laraba wanda ke matsayin ladan sakin fursunonin Isra’ila 16 da Hamas ta yi.

Wani fitacccen dan fafutuka a yankin Falasdinu Ahed Tamimi na cikin fursunoni 30 da Isra’ilan ta saki a jiya, dan fafutukar da ya yi suna a shekarar 2017 bayan zabgawa wani Sojan Isra’ila mari.

Wannan mataki na zuwa ne a dai dai lokacin da Antony Blinken ke Shirin kai ziyara a Tel Aviv yau Alhamis.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.