Isa ga babban shafi

Halin da ake ciki kan yakin Isra'ila da Hamas a Gaza

Isra’ila ta ci gaba da ruwan bama-bamai a yankin Gaza a ranar Lahadin nan, a dai-dai lokacin da kasashen duniya suka kara matsa lamba wajen kare fararen hula da kuma sabunta yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin kasar da kungiyar Hamas.

Daya daga cikin wuraren da Isra'ila tayi wa ruwan bama-bamai ke nan a yankin Gaza.
Daya daga cikin wuraren da Isra'ila tayi wa ruwan bama-bamai ke nan a yankin Gaza. AFP - SAID KHATIB
Talla

Akalla mutane 13 suka mutu ciki harda mata da kananan yara, sannan wasu da dama suka jikkata, a wasu hare-hare da Isra’ila ta kai gidajen da ke sansanin ‘yan gudun hijirar Nurseirat, wanda ke tsakiyar Gaza.

Kamfanin Dillancin Labaran Falasdinu Wafa ya ruwaito cewar wadanda suka jikkata an garzaya da su asibitin al-Awda don ceto rayuwarsu, yayin da wasu da dama ke makale a karkashin burabuzai.

A cewar mazaunan yankin da lamarin ya faru, Isra’ila ta yi amfani da jiragen yakinta ne wajen kai hare-haren, da ake ganin adadin wadanda suka mutu sanadiyarsa ya karu.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce, manufar Isra'ila na kawar da kungiyar Hamas ta Falasdinu na iya daukar kasar tsawon shekaru.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron a lokacin da yake gabatar da taron manema labarai a wajen taron sauyin yanayi na Majalisar Dinkin Duniya Cop28 a Dubai.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron a lokacin da yake gabatar da taron manema labarai a wajen taron sauyin yanayi na Majalisar Dinkin Duniya Cop28 a Dubai. AFP - LUDOVIC MARIN

A lokacin wani taron manema labarai da ya gabatar a wajen taron Majalisar Dinkin Duniya kan sauyin yanayi na COP28 a Dubai, ya ce lokaci yayi da Isra’ila za ta fayyace manufar da take son cimma a yakin.

"Mene ne rugujewar Hamas baki daya, kuma akwai wanda ke ganin zai yiwu? Idan haka ne yakin zai dauki shekaru 10."

Itama mataimakiyar shugabar Amurka Kamala Harris, ta ce Falasdinaw fararen hula da dama sun rasa ransu a wannan yaki, inda shima sakataren harkokin tsaron kasar Lloyd Austin ya ce akwai bukatar Isra’ila ta rinka baiwa fararen hula kariya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.