Isa ga babban shafi

Masu neman shugabancin majalisar Najeriya sun amince da tsayar da mutum guda

‘Yan takara guda 7 da ke neman shugabancin majalisar makilan Najeriya sun yanke hukuncin gabatar da mutum guda domin kalubalantar Tajudden Abbas da suka ce jam’iyyar APC ta dora musu ba tare da amincewar su ba. 

Taron masu neman shugabancin majalisar wakilan Najeriya
Taron masu neman shugabancin majalisar wakilan Najeriya © Twitter/Ahmad Idris Wase
Talla

Bayan wani taro da suka gudanar a karshen wannan mako, ‘yan takaran wadanda daukacin su sun fito ne daga jam’iyyar APC sun ce sun yi haka ne bayan ganawar da suka yi da wani bangare na ‘yan majalisun jam’iyyar PDP wadda ita ce jam’iyya ta biyu mafi girma a majalisar.

Wadannan ‘yan takara sun hada da mataimakin shugaban majalisar wakilai Ahmed Idris Wase da Muktar Betara da Sada Soli Jibia da Aminu Jaji da Yusuf Gagdi da kuma Miriam Onouha.

Yayin da yake magana a madadin ‘yan takaran, Hon Sada Soli ya ce nan gaba kadan za su sanar wa duniya wanda suka amince da shi ya tsaya takarar shugabancin, kuma daukacinsu sun amince su mara masa baya.

Dan majalisar ya ce ba za su bada kai bori ya hau ba wajen nada musu shugabannin daga wajen majalisa, inda ya kara da cewa za su sanar da wanda su ka zaba a wannan mako mai kamawa.

Shi ma dan majalisa Yusuf Gadgi ya tabbatar da wannan matsayi a sanarwar da ya raba wa manema labarai, ba tare da bayyana sunayen wadanda za su tsaya takarar ba. 

Gagdi ya ce sun dauki wannan matsayi ne domin toshe duk wata kofa da ake iya amfani da ita daga wajen majalisar domin nada wadanda za su jagorance su. 

Tuni dai wadannan ‘yan takara suka gabatar da korafinsu ga shugabannin jam’iyyar APC dangane da zabin da ta ce ta yi na wadanda za su rike shugaban majalisar tasu. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.