Isa ga babban shafi

Obasanjo ya bukaci soke zaben shugabancin Najeriya

Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya bukaci a soke zaben shugaban kasar da akayi a karshen mako a yankunan da aka samu tashin hankali. 

Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo, yayin halartar taron tattalin arzikin duniya kan Afirka a Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha, Mayu 11, 2012.
Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo, yayin halartar taron tattalin arzikin duniya kan Afirka a Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha, Mayu 11, 2012. © REUTERS/Tiksa Negeri
Talla

Yayin tsokaci akan zaben, Obasanjo yace rahotanni sun nuna yadda aka samu matsaloli a wasu yankunan, kuma gabatar da sakamakon sun a iya haifar da tashin hankali. 

Tsohon shugaban ya kuma zargi wasu jami’an hukumar zaben da tafka magudi wajen sauya alkaluman zaben da akayi kafin kai sakamakonsa inda aka tsara. 

Obasanjo ya shaidawa shugaba Muhammadu Buhari da a soke zaben domin sake gudanar da shi a ranar 4 ga watan gobe dan kaucewa jefa kasar cikin rikici. 

Tsohon shugaban na daya daga cikin wadanda suke goyan bayan takarar Peter Obi kamar yadda ya bayyana a watan Janairun da ya gabata. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.