Isa ga babban shafi

Majalisar dokokin Najeriya za ta yi bincike kan yadda jami'in Binance ya tsere

Majalisar Wakilan Najeriya ta sanar da fara bincike dangane da yanayin da ke tattare da tserewar wani babban jami'in kamfanin hada-hadar ƙudi ta yanar gizo Binace, Nadeem Anjarwalla, daga inda ake tsare da shi a Abuja cikin watan Maris.

Shugaban kamfanin Binance mai kula da Afirka- Nadeem Anjarwalla
Shugaban kamfanin Binance mai kula da Afirka- Nadeem Anjarwalla © Nigerian government
Talla

A ranar Laraba aka gabatar da kudurin bukatar gudanar da binciken biyo bayan cece-kucen da aka kwashe makonni ana yi kan tserewar Anjarwalla tare da ficewa daga ƙasar.

A watan Maris ne hukumomin Najeriya suka kama Anjarwalla tare da wani babban jami’in Binance, Tigran Gambaryan, bisa zarginsu da laifin halasta kudaden haramun da wasu laifuffuka da suka shafi kudi da kuma tsaro.

Yayin da Gambaryan ke ci gaba da kasancewa tsare, sai kwasam Anjarwalla ya tsere a wani mataki na ba zata da ake alakantawa da baiwa masu gadinsa na goro.

Ba'a kama shi a Kenya ba

A baya akwai rahotanni cewa an yi nasarar kame Jami'in a ƙasar Kenya, sai dai hukumomin kasar sun karyata wannan batu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.