Isa ga babban shafi
Najeriya

Kamata yayi a daure yawancin masu neman shugabancin Najeriya – Obasanjo

Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo, ya ce yawancin ‘yan siyasar da ke neman kujerar shugabancin kasar a zaben shekara ta 2023, kamata yayi su kasance garkame a gidan yari.

Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo, yayin halartar taron tattalin arzikin duniya kan Afirka a Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha, Mayu 11, 2012.
Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo, yayin halartar taron tattalin arzikin duniya kan Afirka a Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha, Mayu 11, 2012. © REUTERS/Tiksa Negeri
Talla

Obasanjo ya bayyana haka ne, a lokacin da yake jawabi wurin bikin cikarsa shekaru 85 da haihuwa a garin Abeokuta da ke jihar Ogun.

Tsohon shugaban Najeriyar da ya ki bayyana sunayen ire-iren mutanen da yake nufi, ya ce miyagun ba za su rika yawo cikin walwala ba, idan har hukumomin yaki da cin hanci da rashawa sun yi aikinsu yadda ya kamata, tare da samun goyon bayan bangaren shari’a.

Yanzu haka dai, wadanda ke kan gaba a tsakanin wadanda suka bayyana aniyar neman hawa kujerar Shugabancin Najeriya a zabe mai zuwa, sun hada da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, da tsohon gwamnan Legas, Ahmed Bola Tinubu, da kuma tsohon shugaban majalisar dattawan Najeriya Bukola Saraki.

Bikin na zagayowar ranar haihuwar tsohon shugaba Obasanjo ya samu halartar manyan baki cikinsu har da shugabar Hukumar Kasuwanci ta Duniya WTO Dakta Ngozi Okonjo-Iweala, da kuma shugaban bankin raya kasashen Afirka AFDB Dakta Akinwumi Adesina.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.