Isa ga babban shafi
Najeriya-Obasanjo

Najeriya na bukatar karin 'yan tawaye don samun ci gaba- Obasanjo

Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya ce kasar na bukatar mutanen da ake kira ‘yan tawaye da dama wadanda za su dinga bayyanawa shugabannin gaskiya ba tare da wata fargaba ba.

Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo.
Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo. AP - Jerome Delay
Talla

Tsohon shugaban da ya ce babu yadda za a yi kasar ta ci gaba muddin kowa na zuba idon sa wajen kallon abinda ke faruwa ba tare da bude baki ana magana ba, ya bayyana damuwa akan yadda Najeriya ta samu kan ta ayau.

Obasanjo ya ce ya zama wajibi ga duk wani mutum da ya tsayawa gaskiya da amana a dinga ganin sa kamar dan tawaye saboda yadda zai dinga tsage gaskiya yana fadawa kowa.

Tsohon shugaban ya ce ba su da wata kasa da za su kira a matsayin ta su, saboda haka suna bukatar karin 'yan tawaye wadanda za su dubi idanun shugabanni domin fada musu gaskiya ba tare da wata fargaba ba.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito Obasanjo na wadannan kalamai ne wajen kaddamar da wani litaffi da aka wallafa akan shugaban addinin kasar Yarbawa Tayo sowunmi a birnin Abeokuta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.