Isa ga babban shafi
Najeriya

Ba zan koma jam'iyyar PDP ba - Obasanjo

Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya bayyana ya sake jaddada cewar ba zai janye matakinsa na ficewa daga jam’iyyar PDP da kuma tsarin siyasar bangaranci ba.

Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo yayin ziyara aiki a Goma dake gabashin Congo, 15/11/2008
Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo yayin ziyara aiki a Goma dake gabashin Congo, 15/11/2008 AP - Jerome Delay
Talla

Obasanjo ya bayyana haka ne, bayan da ya karbi bakuncin shugaban PDP na Najeriya Iyorchia Ayu da sauran masu ruwa da tsaki na babbar Jam’iyyar adawar da suka ziyarce shi ranar Asabar a gidansa da ke Abeokuta, a jihar Ogun.

Obasanjo, wanda ya shugabanci Najeriya kan wa’adi biyu daga shekarar 1999 zuwa 2007 a karkashin  PDP, ya fice daga jam’iyyar ne, bayan da dangantaka ta yi tsami tsakaninsa da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan yayin da ake shirin zabukan shekarar 2015.

Bayan babewa da tsohon shugaba Jonathan ne, Obasanjo ya kekketa katin shaidarsa na zama dan jam’iyyar PDP, tare da shelar barin siyasar bangaranci baya ga ficewar da yayi daga jam’iyyar mai mulki a waccan lokaci.

Shugaba Buhari tare da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo da tsohon shugaban kasa na mulkin soja Janar AbduSalam Abubkar, yayin da dukkansu ke halartar wani babban taron kungiyar Tarayyar Afirka karo na 30 da ake gudanarwa a Addis Ababa.
Shugaba Buhari tare da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo da tsohon shugaban kasa na mulkin soja Janar AbduSalam Abubkar, yayin da dukkansu ke halartar wani babban taron kungiyar Tarayyar Afirka karo na 30 da ake gudanarwa a Addis Ababa. Femi Adesina/Facebook

A shekarun baya bayan nan, tsohon shugaban Najeriyar ya sha yin tsokaci kan lamurra daban daban da suka shafi Najeriya da kuma kamun laudayin gwamnati mai a karkashin jagorancin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, musamman akan batutuwan tsaro da siyasa da kuma kyautatuwar tsarin shugabanci.

A karshen shekarar 2021, Obasanjo ya sake jaddada matsayin sa na ci gaba da dorewar Najeriya a matsayin dunkulalliyar kasa sabanin ‘yadda wasu bangarori ke fafutukar ganin sun balle domin kafa kasa ta kan su.

Obasanjo yace a matsayin sa na ‘dan kabilar Yarbawa ba zai taba goyan bayan kafa kasar Yarbawa zalla ba, domin kuwa shi ya amince da ci gaba da zaman Najeriya a matsayin kasa guda.

Tsohon shugaban yace bai taba amfani da kabilar sa wajen neman biyan bukata a Najeriya ba, saboda shi ya amince da cewar Najeriya ta fi karfin kowacce kabila ko addini ko kuma shiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.