Isa ga babban shafi

Zan daukaka kara kan hukuncin kotun korafe-korafen zabe - Atiku

Tsohon Mataimakin shugaban kasar Najeriya Atiku Abubakar ya ce bai gamsu da hukuncin kotun zaben da aka yanke jiya ba dangane da zaben shugaban kasar na watan Fabarairu, saboda haka ya umarci lauyoyinsa su ruga kotun koli domin daukaka kara. 

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya kenan Atiku Abubakar
Tsohon mataimakin shugaban Najeriya kenan Atiku Abubakar © premium times
Talla

Yayin da yake jawabi ga manema labarai dangane da hukuncin kotun, Atikun ya ce hukuncin kotun ya ba shi mamaki, duk da yake bai kauda imanin da yake da shi ga bangaren shari’a wajen yin adalci ga wadanda aka takewa hakki ba. 

Atiku ya ce shi ba bakon kotu ba ne, lura da irin shari’un da ya yi ta tafkawa, kuma ya san yadda kotuna ke aiki, saboda haka ya san kotuna a matsayin madogara ga wadanda aka zalunta. 

Ya kara da cewar wannan hukunci na jiya zai bada damar kawar da fatan da ake da shi na dorewar dimokiradiya da kuma wanzar da adalaci a tsakanin al’umma. 

‘Dan takarar jam’iyyar PDPn ya ce ganin yadda alkalan suka yi watsi da tanade-tanaden dokokin zabe da kuma irin shaidun da suka gabatar musu, ya umarci lauyoyinsa da su aiwatar da ’yancin da dokar kasa ta ba shi na daukaka kara. 

Atiku ya bayyana hukuncin a matsayin koma-baya ga dimokiradiya, wanda ya ce ya shafi daukacin ‘yan siyasa ne ba tare da la’akari da jam’iyyar da suka fito ba. 

Tsohon mataimakin shugaban ya kuma bayyana jam’iyyar PDP a matsayin uwa ga daukacin ‘yan siyasar Najeriya saboda gudumawar da ta bayar wajen gina dimokiradiyar da ake cin gajiyarta a wannan lokaci, yayin da ya bukaci magoya bayansa da su kwantar da hankalinsu wajen ganin sun bi kadin hakkinsu a kotun koli. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.