Isa ga babban shafi

Kotu ta karbe kujerar Dan Majalisar Wakilai a Kano ta bai wa Kwankwaso

Kotun da ke sauraron kararrakin zabe a Kano da ke Najeriya, ta kwace kujerar Dan  Majalisar Tarayya daga hannun Datti Yusuf Umar na jam'iyyar NNPP, inda ta bayyana Musa Ilyasu Kwankwaso na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya samu nasara a mazabar Kura da Madobi da Garun Malam. 

Ginin Maljalisar Dokokin Najeriya.
Ginin Maljalisar Dokokin Najeriya. AFP - KOLA SULAIMON
Talla

 

Kotun ta tabbatar da zargin cewar Umar bai ajiye aikin sa a Jami’ar Bayero ba kwanaki 30 kafin gudanar da zabe, kamar yadda doka ta tanada. 

Mai shari’a Ngozi Flora Azinge ta umarci hukumar zabe ta INEC da ta karbe shaidar nasarar zaben da aka bai wa Yusuf Umar na jam’iyyar NNPP domin mika wa Ilyasu Musa Kwankwaso na jam’iyyar APC wanda ya zo na biyu a zaben da aka yi ranar 25 ga watan Fabarairun wannan shekara. 

Idan dai ba’a manta ba Umar ne ya samu kuri’u mafi yawa a saben kujerar majalisar tarayyar da aka yi, abin da ya sa hukumar zabe ta bayyana shi a matsayin zababben ‘dan Tajalisar Tarayya daga jihar kano. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.