Isa ga babban shafi

Tashin hankalin Burkina Faso ya raba mutane da gidajensu

Bayanai daga Togo na cewa hare-haren ta’addanci a makwafciyar kasar Burkina Faso ya yi sanadin raba mutane fiye da dubu 4 da muhallan su.

Taswirar Burkina Faso
Taswirar Burkina Faso © RFI
Talla

Rahotanni sun tabbatar da cewa a jimlace iyalan gidaje dari 789 da suka kunshi mutane dubu 4 da 175 ne suka tsere daga muhallan su, tare da komawa wasu yankunan kamar dai yadda ministan yada labaran gwammantin Togo Akodah Ayewouadan ya bayyana.

Kasar Togo da ke makwaftaka da Jamhuriyar Benin da Ghana da kuma Ivory Coast na fuskantar baranazar fantsamar hare-haren ta’addanci.

Mali, Burkina Faso da Nijar na fama da tashe-tashen hankula na masu ikirarin jihadi da makwaftan kasashe,da suka shafe shekaru da dama suna nuna damuwa game da tashe-tashen hankula da suka mamaye yankunansu.

A tsakiyar watan Yuli ne aka kai wa Togo hari da  wasu  mayaka dauke da makamai da ba a san ko su waye ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.