Isa ga babban shafi

Sojoji uku da wasu fararen hula 8 suka mutu a wani harin kwantar bauna a Burkina Faso

A Burkina Faso,mayakan jihadi sun kashe akalla sojoji uku da wasu fararen hula 8 a wani harin kwantar bauna da suka kai jiya asabar a gundumar Bouroum da ke arewacin kasar, kamar yadda majiyoyin tsaro suka shaida wa kamfanin dillancin labarai Faransa na AFP.

Dakarun kasar Burkina faso
Dakarun kasar Burkina faso © Olympia De Maismont / AFP
Talla

 

Wata majiya da ke tabbatar da harin, ta ce adadin na iya karuwa. Majiyar ta ce an kai harin ne a kusa da Silmangue, a lardin Namentenga.

Harin na baya-bayan nan ya zo ne bayan juyin mulkin ranar 30 ga watan Satumba da ya hambarar da Laftanar-Kanar Paul-Henri Sandaogo Damiba, wanda shi kansa ya kwace mulki a watan Janairu ,da kwana guda bayan da aka nada kaftin din Ibrahim Traore mai shekaru 34 a matsayin wanda zai gaje shi a matsayin shugaban rikon kwarya.

Daya daga cikin kasashe mafi talauci a duniya, Burkina Faso na da tarihin juyin mulki tun bayan samun 'yancin kai daga Faransa a 1960.

Dubban mutane ne aka kashe tare da raba kusan miliyan biyu da muhallansu .Kyaftin Traore ya sha alwashin tabbatar da alkawarin da Damiba ya yi na komawa gwamnatin farar hula nan da watan yulin 2024 a karshe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.