Isa ga babban shafi

Burkina Faso za ta zabi shugaban rikon kwarya gabanin mika mulki ga farar hula

Sojojin da suka yi juyin mulki a Burkina Faso sun sanar da cewar a makon gobe za a gudanar da wani taron da zai bada damar zaben shugaban gwamnatin rikon kwaryar da zai jagoranci kasar zuwa lokacin zabe.

Jagoran mulkin Soja a  Burkina Faso, Kaftin Ibrahim Traoré.
Jagoran mulkin Soja a Burkina Faso, Kaftin Ibrahim Traoré. AFP - -
Talla

Wata doka da shugaban sojin da suka jagoranci juyin mulki Kaftin Ibrahim Traore ya gabatar, ya ce ganin yadda aka amince da shirin mika mulki ga fararen hular, a ranar 14 da 15 ga wannan wata, za a gudanar da taro na kasa wanda zai bada damar zaben shugaban kasa.

Traore mai shekaru 34 ya jagoranci abokan aikinsa wajen kifar da Laftanar Kanar Paul Henri Sandaogo Damibia daga karagar mulki abinda ya sanya shi ya zama shugaban kasa mafi karancin shekaru a tarihi.

Karo na 2 kenan Burkina Faso na ganin juyin mulkin Soja cikin watanni 8 dai dai lokacin da al'amuran tsaro suka damalmale a kasar sakamakon karuwar hare-haren kungiyoyi masu ikirarin jihadi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.