Isa ga babban shafi

Hankula sun kwanta a Burkina Faso bayan ficewar Damiba zuwa Togo

Hankula sun kwanta a Burkina Faso bayan hambararren shugaban kasar na mulkin Soja Kanal Paul-Henri Sandaogo Damiba ya samar damar tserewa tare da samun mafaka a Togo.

Sabon shugaban mulkin Sojan Burkina Faso, Kaftin Ibrahim Traore.
Sabon shugaban mulkin Sojan Burkina Faso, Kaftin Ibrahim Traore. AFP - IDRISSA OUEDRAOGO,ADAMA OUEDRAOGO
Talla

Tsawon kwanaki 3 aka shafe cikin rudani a Burkina Faso bayan sanya dokar hana fita da ta kai ga dakatar da duk wata hada-hada yayinda aka katse sadarwar gidajen radio da talabijin.

A wani sakon bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook jiya litinin, Damiba da ya jagoranci kasar tsawon watanni 8 biyo bayan juyin mulkin da ya yi ga gwamnatin shugaban farar hula Roch Marc Christian Kabore, ya bayyana dalilin da suka sanya shi barin gwamnati yayinda ya ce yanzu haka ya samu mafaka a Togo.

Damiba ya yi ikirarin cewa da radin kansa ne ya zabi ajje mukamin nasa na shugaban rikon kwarya bayan tattaunawar fahimtar juna tsakaninsa da shugabannin gargajiya da na addini da kuma shugaban kungiyar ECOWAS bay ga shi kansa Kaftin Ibrahim Traore.

Damiba ya karkare jawabin nasa da fatan alkhairi ga Burkina Faso.

Jagoran mulkin Sojan na Burkina Faso, Ibrahim Traore ya sha alwashin mika mulki ga fararen hula nan da watanni 24 kamar yadda aka tsara tsakanin tsohon shugaban mulkin Sojan kasar da kungiyoyin AU da ECOWAS.

Yau talata ake saran ziyarar wakilcin kungiyar ECOWAS a kasar ta Burkina Faso don tattaunawa da sabon jagoran Sojin kasar Kaftin Ibrahim Traore.

Wasu hotuna da aka wallafa a shafukan sada zumunta sun nuna yadda al'ummar kasar suka yi dandazon taya murna ga sabon jagoran galibinsu rike da tutar Burkina Faso.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.