Isa ga babban shafi

Ibrahim Traore: matashin jagoran juyin mulkin Burkina Faso mai shekaru 34

Bayanai na cewa, yaro ne mai kunya amma haziki a makaranta, Kyaftin din Burkina Faso Ibrahim Traoré ya zama jami'in soji na baya-bayan nan da ya kwace mulki a wani juyin mulki a daya daga cikin kasashen da Faransa ta yi wa mulkin mallaka a yammacin Afirka.

Sabon shugaban gwamnatin sojin Burkina Faso kenan wato Ibrahim Traore
Sabon shugaban gwamnatin sojin Burkina Faso kenan wato Ibrahim Traore © AFP
Talla

An haife shi a shekara ta 1988, wannan ya sa kyaftin din mai shekaru 34 ya zama shugaban kasa mafi karancin shekaru a Afirka, inda ya shiga cikin jerin wasu jagororin juyin mulkin guda biyu masu kwarjini, Mamady Doumbouya na Guinea, wanda aka haife shi a 1981, da Kanal Assimi Goïta na Mali, wanda aka haifa a 1983. .

Watanni takwas bayan juyin mulkin da ya gabata, Kyaftin Ibrahim Traoré ya gaji Laftanar Kanal Sandaogo Damiba a matsayin shugaban Burkina Faso.

Amma shin ya kamata a kalli hakan a matsayin alamar kaddara? Dan shekaru 34, Ibrahim Traoré ya zama sabon shugaban Burkina Faso, yana da shekaru daya da Thomas Sankara, wanda ya karbi ikon kasar a tsakiyar 1980. Yanzu haka Kyaftin Ibrahim Traoré yana matsayin shugaban Burkina Faso.

Juyin mulkin nasa - karo na biyu a Burkina Faso cikin kasa da watanni tara, shi ne alama ta baya-bayan nan ko kuma irin juyin mulkin da shugaban Majalisar Dinkin Duniya António Guterres ya nuna damuwa a kai a 2021.

Sai dai ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da gidan rediyon RFI cewa ya shiga wannan matsayi domin karawa sojojin kaimi wajen tunkarar matsalolin da suka dabaibaye kasarsa.

Har ya zuwa yanzu, Ibrahim Traoré, shi ne babban hafsan soji na runduna ta 10 da ke da hedkwata a Kaya. Ya shugabancin rundunar Patriotic Movement bayan faduwar Laftanar-Kanar Paul-Henri Damiba.

Ibrahim Traoré ya yi karatu a Jami'ar Ouagadougou a shekara ta 2006, ya kammala karatun digirinsa na farko a fannin ilimin kasa.

Bayan shekaru uku da kammala karatu, sai ya yanke shawarar shiga aikin soja. A cikin shekarar 2010 ne aka dauke shi aiki a Kwalejin Soja ta Georges Namoano a Pô, wanda ke da cibiyar horar da kwamandojin soji.

Tawagar da tayi juyin mulkin da ya gabata

Bayan shekaru biyu yana karbar horo, an tura matashin Laftanar din na biyu zuwa rundunar sojojin da ke Kaya a yankin tsakiyar-Arewa.

A cikin shekarar 2014, ya samu karin girma zuwa laftanar kuma, a cikin 2020, ya kakin da ke dauke da ratsin kyaftin dinsa.

An nada Kyaftin Ibrahim Traoré a matsayin babban hafsan soji na runduna ta 10 da ke Kaya a watan Maris din da ya gabata karkashin Laftanar-Kanar Paul-Henri Sandaogo Damiba.

Yana daya daga cikin matasan hafsoshin da suka hambarar da Roch Marc Christian Kaboré a ranar 24 ga watan Janairu. Bugu da kari, Kyaftin Ibrahim Traoré ya himmatu wajen yaki da kungiyoyin masu dauke da makamai a kasar.

A cewar ‘yan uwansa, yakan ziyarci mutanensa a lokacin da yake aikin tsaro.

Ibrahim Traoré ya karbi horo na musamman, tare da rukunin kwamandojin Pô a Morocco. Sunan da sojoji ke kiran sa da shi shine, masanin kimiyya da fasaha, ana mutunta shi a cikin dakarun yaki saboda jajircewarsa da kuma kusancinsa da sojojin da yake aiki tare da su.

Amma Kyaftin Traoré ba janar din yaki ne da aka yi wa ado ba, sai dai kyaftin din da ya yi karatu a wata makarantar soji, ya shiga aikin soja a shekara ta 2009 kuma ya samu horon harbin bindiga a Morocco.

Ba kamar wanda ya gabace shi ba, yana kawo shawarwarin da suka shafi ci gaba sosai, in ji wata majiya mai alaka da sojojin. Soja ne mai daraja wanda ya samu mukami bisa cancantarsa.

Bisa rashin ingancin tsarin dimokuradiyya a kasar da sojoji suka dade suna rike da madafun iko, Kyaftin Traoré ya kwace mulki tare da yin alkawarin inganta tsaro a kasar da ke cikin fargabar 'yan ta'adda.

Yayin da manyan kasashen duniya suka mayar da hankali ko dai kan rikicin cikin gida, ko kuma yakin Ukraine, sun gaza mai da hankali sosai kan rashin zaman lafiya da ya dabaibaye kasashe irin su Burkina Faso.

Kalaman Ibrahim Traoré na nuni da cewa, zai iya yin koyi da takwaransa na kasar Mali, wanda ake zargin ya kawo sojojin hayar Rasha na Wagner mai cike da cece-kuce, domin maye gurbin dakarun faransa a yakin da ake yi da masu tayar da kayar baya, duk kuwa da cewa ba a samu nasara ba, ganin yadda 'yan tawayen suka kara tsananta a can ma. tun bayan da sojoji suka yi juyin mulki a watan Agustan 2020.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.