Isa ga babban shafi

Al'ummar Burkina Faso sun yi zanga-zangar bukatar shigowar Rasha kasar

Dubunnan al'ummar Burkina Faso dauke da tutar kasar Rasha sun gudanar da zanga-zanga a Ouagadougou babban birnin kasar a jiya talata, a wani yunkuri da ke nuna bukatarsu ga kawo sojojin Moscow kasar don yakar ayyukan ta'addanci.

Zanga-zangar goyon bayan Rasha a Burkina Faso.
Zanga-zangar goyon bayan Rasha a Burkina Faso. © AP/Kilaye Bationo
Talla

Zanga-zangar wadda ke zuwa a dai dai lokacin da tawagar wakilan kungiyar ECOWAS karkashin jagorancin ministan harkokin wajen Guinea-Bissau Suzi Carla Barbosa ke kammala  ziyarar a kasar, kwanaki bayan juyin mulki karo na biyu cikin kasa da watanni 9.

Dubunnan al'ummar ta Burkina Faso, sun rika daga tutar Rasha yayin zanga-zangar ta jiya, wadda suka gudanar da nufin nuna goyon baya ga sabuwar gwamnatin Sojin kasar karkashin jagorancin Ibrahim Traore don ganin ta kwaikwayi makwabciyar kasar a kokarin shigo da Sojin Rasha kasar don yakar ayyukan ta'addanci.

Masu zanga-zangar sun rika furta kalaman bukatar ficewar Faransa daga kasar, baya ga gargadin kungiyar ECOWAS daga yi musu shisshigi a harkokin tafiyar da sabuwar gwamnatin.

A juma'ar da ta gabata ne Kaftin Ibrahim Traore, matashin Soja mai shekaru 34 ya jagoranci juyin mulkin da ya hambarar da Laftanar-Kanar Paul-Henri Sandaogo Damiba wanda ya kwace mulki daga Roch Marc Christian Kabore a watan Janairu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.