Isa ga babban shafi

Ana cikin halin rudani a Burkina Faso bayan juyin mulkin Soji

An shiga halin tantama da rudani a Burkina Faso bayan juyin mulkin Soji na 2 cikin watanni 8 lamarin da ya hambarar da gwamnatin Sojin Laftanal Kanal Paul Henri Sandaogo Damiba, bayan zarginsa da gaza daukar matakan da suka dace wajen magance matsalolin hare-haren ta’addancin da kasar ke fuskanta.

Tawagar Sojin Burkina Faso da suka jagoranci juyin mulki a kasar.
Tawagar Sojin Burkina Faso da suka jagoranci juyin mulki a kasar. © RTB / Capture d'écran
Talla

An dai bayyana sunan Kaftin Ibrahim Traore mai shekaru 34 a matsayin wanda ya jagoranci juyin mulkin na jiya juma’a, wanda ya sanar da juyin mulkin saboda karuwar hare-haren ta’addanci ba tare da daukar mataki ba.

A jawabin da suka gudanar ta gidan talabijin, tawagar Sojin da suka jagoranci juyin mulkin karkashin jagorancin Kaftin Ibrahim, sun ce gwamnatin Damiba ta gaza wajen magance matsalolin tsaron da kasar ke fuskanta ta yadda aka fara ganin hare-haren ta’addanci hatta a yankunan da a baya ‘yan ta’adda basa iya zuwa.

Har yanzu dai akwai tarin dakarun Soji baje a kusan dukkanin titunan birnin Ouagadougou yayinda aka sanya dokar hana fita a sassan birnin, a bangare guda kuma Sojoji ke ci gaba da tsare gidajen talabijin da na Radiyo.

Haka zalika an dakatar da dukkanin hada-hada musamman shagunan cinikayya inda suka ci gaba da kasancewa a kulle yau asabar.

Tuni dai kungiyar ECOWAS ta yi tir da juyin mulkin Sojin na Burkina Faso wanda ta bayyana da abin kunya a dai dai lokacin da ake shirin mayar da kasar karkashin mulkin demokradiyya nan da ranar 1 ga watan Yulin shekarar 2024.

Faransa da ke matsayin uwar goyon kasar ta yammacin Afrika, ta bukaci al’ummarta da ke cikin birnin Ouagadougou da aka yi ittifakin sun kai dubu 4 zuwa 5 su ci gaba da zama a gidajensu don kaucewa fuskantar matsala yayinda Tarayyar Turai ta bukaci kwantar da hankula a bangare guda Amurka ta bukaci fahimtar juna daga bangarorin biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.