Isa ga babban shafi

An shiga fargaba a Burkina Faso bayan jiyo karar harbe-harbe a fadar shugaban kasa

Wasu rahotanni daga Burkina Faso sun ce an jiyo karar musayar harbe-harben bindiga a gab da fadar shugaban kasar da ke birnin Ouagadougou a safiyar yau juma’a.

Laftanal kanal Paul Henri Sandaogo Damiba.
Laftanal kanal Paul Henri Sandaogo Damiba. © RTB via AP
Talla

Tun da sanyin safiyar yau juma’a aka ga tarin jami’an tsaro a gab da shalkwatar rundunar Sojin kasar yayinda aka kakkafa shingayen binciken a kusan dukkanin manyan titunan babban birnin na Burkina Faso.

Kamfanin dillancin labaran Faransa, ya ruwaito cewa ilahirin gidajen talabijin da na radiyo basa aiki a sassan kasar.

Makamancin wannan hali ne dai aka shiga a watan Janairu lokacin da Sojoji karkashin jagorancin Laftanal Kanal Paul-Sandaogo Damiba suka yi juyin mulkin a kasar.

Rahotanni sun ce al’ummar kasar na cikin halin dar-dar tare da fargabar yiwuwar fuskantar juyin mulki ko wani abu makamancin haka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.