Isa ga babban shafi

Harin ta'addanci ya yi sanadin mutuwar mutane 4 a Burkina Faso

Rundunar sojin Burkina Faso ta ce sojojinta akalla biyu da kuma wasu jami’an tsaron sa-kai na farar hula biyu ne suka rasa rayukansu, a wani hari da ‘yan ta’adda suka kai kan tawagarsu da ke sintiri.

Wasu sojojin  Burkina Faso da ke sintiri a birnin Ouagadougou.
Wasu sojojin Burkina Faso da ke sintiri a birnin Ouagadougou. © Olympia de Maismont / AFP
Talla

Sanarwar rundunar sojin, ta ce an ‘yan ta’addan sun yi wa hadin gwiwar sojoji da ‘yan sa-kan kwanton baunar ne a ranar Asabar, a tsakanin garuruwan Sakoani da Sampieri da ke lardin Tapoa mai iyaka da kasashen Nijar da Benin.

Sai dai wata majiyar tsaro ta shaidawa kamfanin dilancin labarai na AFP cewa adadin wadanda suka mutun sojoji hudu ne da kuma masu aikin sa-kai biyu.

Wata majiyar tsaron kuwa ta tabbatar da cewa su ma mayaka masu ikirarin jihadin sun yi asara, ba tare an bayyana adadin wadanda aka kashe daga cikinsu ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.