Isa ga babban shafi

Harin 'yan ta'adda ya kashe fararen hula 35 a arewacin Burkina Faso

Akalla fararen hula 35 ne suka mutu yayinda wasu 37 suka jikkata, sakamakon wani harin bam da aka kai kan ayarin motocin da ke dauke da kayayyaki a arewacin kasar Burkina Faso, yankin da ke fama da hare-haren mayaka masu ikirarin jihadi.

Wani harin 'yan ta'adda a Burkina Faso.
Wani harin 'yan ta'adda a Burkina Faso. AFP - OLYMPIA DE MAISMONT
Talla

An kai harin na ranar Litinin ne a daidai lokacin da ayarin motocin da sojoji ke yi wa rakiya, suke kokarin sayen kayayyakin bukata a wasu garuruwan yankin arewacin kasar ta Burkina Faso, inda daya daga cikin motocin ta taka nakiya a kan hanyar da ke tsakanin Bourzanga zuwa Djibo.

Wata majiyar tsaro ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewar ayarin motocin ya kunshi ‘yan kasuwa ne da kuma sauran fararen hula.

Wani mazaunin garin Djibo, ya ce wadanda abin ya rutsa da su ‘yan kasuwa ne da za su sayi kayayyaki a birnin Ouagadougou da kuma daliban da za su koma babban birnin domin fara sabon zangon karatu.

A baya-bayan nan dai ‘yan ta’adda masu ikirarin jihadi sun kai hare-hare ta hanyar dasa bam a kan titunan da suka hada da manyan biranen arewacin kasar Burkina Faso da suka hada da Dori da Djibo, inda ko a farkon watan Agusta, sojoji 15 suka rasa rayukansu a yankin bayan fashewar bama-bamai biyu.

Burkina Faso ta shafe akalla shekaru 7 tana fama da hare-haren ‘yan ta’adda, wadanda suka yi sanadin mutuwar mutane sama da dubu 2,000 tare da tilastawa wasu mutane miliyan 1.9 barin gidajensu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.