Isa ga babban shafi

Mali ta amince da karfafa huldar soji da Burkina Faso

Shugabannin gwamnatocin kasashen Mali da Burkina Faso sun yanke hukuncin bunkasa dangantakar sojin dake tsakanin su, yayin ganawar da suka yi yau a Bamako.

© MICHELE CATTANI / AFP
Talla

Wannan ya biyo bayan ziyarar aikin da shugaban mulkin sojin Burkina Faso, Laftanar Kanar Paul Henri Sandaogo Damiba ya kai Mali, wadda itace ziyarar sa zuwa kasar waje ta farko tun bayan juyin mulkin da yayi, inda ya tattauna da Kanar Assimi Goita.

Sanarwar bayan taron da shugabannin biyu suka bayar tace sun amince su hada kai domin tinkarar yaki da ta’addancin da ya addabe su.

Kasar Mali ta janye daga rundunar tsaron hadin gwuiwa ta G5 Sahel dake yaki da Yan ta’adda a farkon wannan shekarar, yayin da a watan jiya kasashen Burkina Faso da Mali suka bukace ta da sake tunani akai.

Rahotanni sun ce shugabannin biyu sun kuma tatatuna akan sojojin Cote d’Ivoire da aka tsare a Mali, wadanda ake zargin cewar sojojin haya ne da suka shiga kasar ba tare da izini ba.

A jiya Asabar, gwamnatin Mali ta saki mata 3 daga cikin sojojin Cote d’Ivoiren da ta tsare.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.