Isa ga babban shafi

Mali da Burkina Faso sun amince su bunkasa huldarsu ta soji

Shugabannin mulkin sojin kasashen Mali da Burkina Faso sun tsayar da shawarar bunkasa dangantakar sojin da ke tsakaninsu yayin ganawar da suka yi a Bamako.

Damiba da Goita
Damiba da Goita © The Maravi Post
Talla

Wannan ya biyo bayan ziyarar aikin da shugaban mulkin sojin Burkina Faso, Laftanar Kanar Paul Henri Sandaogo Damiba ya kai Mali, wadda ita ce ziyararsa zuwa kasar waje ta farko tun bayan juyin mulkin da ya yi, inda ya tattauna da Kanar Assimi Goita.

Sanarwar bayan taron da shugabannin biyu suka bayar ta ce, sun amince su hada kai domin tinkarar yaki da ta’addancin da ya addabe su.

Kasar Mali ta janye daga rundunar tsaron hadin gwuiwa ta G5 Sahel da ke yaki da 'yan ta’adda a farkon wannan shekarar, yayin da a watan jiya kasashen Burkina Faso da Mali suka bukace ta da sake tunani akai.

Rahotanni sun ce, shugabannin biyu sun kuma tattatuna akan sojojin Cote d’Ivoire da aka tsare a Mali, wadanda ake zargin cewar sojojin haya ne da suka shiga kasar ba tare da izini ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.