Isa ga babban shafi

Burkina Faso ta kori ministan tsaro bayan tsanantar hare-haren ta'addanci

Gwamnatin Sojin Burkina Faso karkashin jagorancin Laftanal Kanal Paul-Henri Sandaogo Damiba ta sanar da korar ministan tsaron kasar Janar Barthelemy Simpore, biyo bayan tsanantar hare-haren ta’addanci a sassan kasar.

Laftanal Kanal Paul-Henri Damiba, jagoran gwamnatin Sojin Burkina Faso.
Laftanal Kanal Paul-Henri Damiba, jagoran gwamnatin Sojin Burkina Faso. © OLYMPIA DE MAISMONT/AFP
Talla

Cikin wasu kunshin doka guda biyu da gwamnatin Sojin ta fitar a yammacin jiya litinin ta bayyana matakin korar ministan tsaron a sadarar doka ta farko yayinda doka ta biyu ke bayyana jagoran mulkin Sojin kasar Laftanal Kanal Paul-Henri Sandaogo Damiba a matsayin sabon ministan tsaro.  

Sabbin dokokin biyu da aka karanto su kai tsaye ta gidajen talabijin, sun kare matakin jagoran da cewa yunkuri ne na kakkabe barazanar hare-haren ta'addancin da ke ci gaba da ta'azzara a sassan Burkina Faso.

Wannan dai shi ne sauye-sauye na farko da gwamnatin Damiba ke gudanarwa tun bayan rantsar da ita cikin watan Maris.

Shugaban mulkin sojin Burkina Faso Laftanal Kanar Paul-Henri Sandaogo Damiba, wanda ya hambarar da gwamnatin farar hular da Roch Marc Christian ke jagoranta a ranar 24 ga watan Janairun shekarar nan, ya sha alwashin murkushe hare-haren kungiyoyi masu ikirarin jihadin da Burkina Faso ke fama da su.

Tun shekarar 2015 Burkina Faso ke fama da hare-haren 'yan ta'adda wanda ya shiga kasar daga Mali da ke makwabtaka da ita tare da kisan fararen hula akalla dubu 2 baya ga jami'an tsaro inda a bangare guda ya tilastaw mutane miliyan 1 da dubu dari hudu tserewa daga matsugunansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.