Isa ga babban shafi

Damiba ya sha alwashin kawo karshen matsalar ta'addanci a Burkina Faso

Shugaban mulkin sojan Burkina Faso Paul-Henri Sandaogo Damiba ya sha alwashin fatattakar kungiyoyin da ke dauke da makamai, kwana guda bayan da harin bam ya yi sanadin mutuwar mutane da dama.

Laftanal Kanal Paul Henri Sandaogo Damiba shugaban mulkin Sojan Burkina Faso.
Laftanal Kanal Paul Henri Sandaogo Damiba shugaban mulkin Sojan Burkina Faso. © RTB via AP
Talla

Akalla fararen hula 35 ne suka mutu yayin da wasu 37 suka jikkata a ranar litinin, bayan da wani bam ya tarwatsa ayarin motocin da ke dauke da ‘yan kasuwa da dalibai a arewacin kasar ta Burkina Faso.

Harin na ranar litinin na zuwa ne a dai dai lokacin da jagoran Sojan na Burkina Faso ke kammala ziyara a Ivory Coast inda ya tattauna da shugaba Alassane Ouattara dangane da sabbin dabarun yaki da matsalolin tsaron da suka dabaibaye kasar.

Kimanin shekaru bakwai kenan da kasar ta shafe tana fama da hare-haren ‘yan ta’adda, da suka yi sanadin mutuwar mutane sama da 2,000 tare da tilastawa wasu kusan miliyan 2 barin gidajensu.

Fadan dai ya fi karkata ne a yankunan arewaci da Gabashin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.