Isa ga babban shafi

Nijar da Burkina Faso za su yi aikin hadin gwiwa domin yakar ta'addanci

Shugaban kasar Burkina Faso, Kanar Henri Sandaogo Damiba ya ziyarci Jamhuriyar Nijar ayau lahadi, inda ya tattauna da mai masaukin bakinsa, Bazoum Mohammed dangane da batutuwan da suka shafi tsaro akan iyakokin kasar.

Shugaban Burkina Faso Kanar Henri Sandaogo Damiba da shugaban Nijar Bazoum Mohammed
Shugaban Burkina Faso Kanar Henri Sandaogo Damiba da shugaban Nijar Bazoum Mohammed © rfi
Talla

Rahotanni sun ce shugabannin biyu sun amince da cigaba da hadin kai a tsakanin kasashen su wajen samar da tsaro a yankin da ya hada iyakokin Nijar da Mali da Burkina Faso, inda ake fama da matsalar 'yan ta’adda.

Wannan ziyarar na zuwa ne bayan wadda ministan tsaron Nijar, Alkassoum Indatou ya kai Burkina Faso, a ranar 22 ga watan Agusta, inda suka kulla yarjejeniyar soji a tsakanin su.

Nijar da Burkina Faso, na daga cikin kasashen yankin Sahel dake fama da matsalar 'yan ta’adda.

Latsa alamar sauti don sauraron rahoton Baro Arzika daga Yamai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.