Isa ga babban shafi

Yadda sojoji suka kifar da gwamnatin Damiba a Burkina Faso

Jami'an soji sun sanar da tsige shugaban mulkin sojan Burkina Faso a ranar Juma'a, bayan ya gaza kawo karshen ayyukan masu tayar da kayar baya da suka addabi kasar da ke Yammacin Afirka.

Laftanal-kanal Paul-Henri Sandaogo Damiba, tsohon shugaban gwamnatin mulkin sojin Burkina Faso
Laftanal-kanal Paul-Henri Sandaogo Damiba, tsohon shugaban gwamnatin mulkin sojin Burkina Faso AFP - OLYMPIA DE MAISMONT
Talla

An sanar da korar Laftanar-Kanar Paul-Henri Sandaogo Damiba, wanda ya hau kan karagar mulki a watan Janairun da ya gabata a wata sanarwa da aka karanta a gidan talabijin na kasar.

Sojojin da ke tawaye sun kuma sanar da rufe kan iyakokin kasar, da kuma dakatar da kundin tsarin mulkin kasar hadi da rusa tsarin tsohuwar gwamnati.

Yanzu haka dai an ayyana Kyaftin Ibrahim Traore, a matsayin sabon shugaban gwamnatin sojin kasar.

Kimanin sojoji 15 ne suka bayyana a gidajen rediyo da talabijin, kafin karfe 8:00 na dare agogon kasar inda suka karanta sanarwar.

"Mun yanke shawarar daukar nauyin da ya rataya a wuyanmu, bisa manufa guda, maido da tsaro da amincin yankinmu," in ji sanarwar.

An kuma sanar da dokar hana fita daga karfe 9:00 na dare zuwa 5:00 na safe.

Tun da farko, gwamnatin kasar ta ce "rikicin cikin gida" da ke tsakanin sojojin kasar ne ya haddasa tura sojoji a muhimman yankunan babban birnin kasar, kuma ta ce ana ci gaba da tattaunawa bayan harbe-harbe da suka rika tashi kafin wayewar gari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.