Isa ga babban shafi

Juyin Mulki: Nan da yaushe za a samu daidaito a Burkina Faso?

Ta yaya zaman lafiya zai koma Burkina Faso? A karo na biyu cikin watanni 9 kacal, jami'an soji sun samu yabo daga masu zanga-zanga a titunan birnin Ouagadougou bayan kwace iko.

Yadda mutane suka yi gangami bayan juyin mulkin ranar Juma'a a Burkina Faso
Yadda mutane suka yi gangami bayan juyin mulkin ranar Juma'a a Burkina Faso REUTERS - VINCENT BADO
Talla

Juyin mulkin ranar Juma’a dai ya haifar da tofin Allah tsine a wani bangare kuma ya samu kyakkyawan fata. Kamar yadda mai magana da yawun gwamnatin mulkin sojan Guinea ya yi tsokaci kan lamarin.

"Idan muna so mu yi la'akari da sauyin yanayi a Burkina amma ya kamata mu mai da hankali kan ka'idoji kawai ta hanyar cewa juyin mulki abin la'akari ne kuma dole ne a iyakance shi na tsawon lokaci, ba tare da samar da mafita ga abubuwan da ke haifar da wadannan rikice-rikice ba, muna daukar hadarin cewa ya sake faruwa," In ji Ousmane Gaoual Diallo.

“Hukumomin Guinea sun dage cewa yana da muhimmanci a yi tambaya kan yanayin kowace kasa domin kokarin samar da hanyoyin da suka dace don magance matsalolin da wadannan kasashe ke fuskanta.

Batun Burkina Faso ba daya ba ne da na Mali, haka zalika Guinea. Don haka, kowace kasa tana da nata abubuwan da suka dace, da yanayin da ya kamata a yi la’akari da su,” in ji shi.

Tun daga shekarar 2015 ne mayakan jihadi suka bazu zuwa Burkina Faso daga makwabciyarta kasar Mali.

Hambararren shugaban, Kanal Damiba ya karbi ragamar mulkin kasar sakamakon halin rashin tabbas din da kasar ke ciki, inda ya sha alwashin ba da fifiko kan harkokin tsaro.

Kakakin ya ce "Ina ganin batun tsaro, daidaiton yankuna, da yaki da ta'addanci batutuwa ne da a karshe ke tsara duk wani rikici da ke faruwa a Burkina Faso."

"Dole ne mu ba da amsoshi kan wannan, za a iya tallafawa, fadadawa, tare da neman shawarwarin gamayyar kungiyoyin kasa da kasa, da kungiyar ECOWAS, domin baiwa al'ummar Burkina Faso damar komawa cikin yanayin da aka saba na zaman lafiya," in ji shi.

Yayin da Burkina Faso ke jiran dawowar kwanciyar hankali, har yanzu mutane miliyan 2 suna gudun hijira yayin da wasu ke makale a yankunan da 'yan ta'adda ke iko da su.

Sabon jagoran juyin mulkin, Ibrahim Traoré ya ce sojoji ba su da kayan aiki na yau da kullun a karkashin Damiba. Abin jira a gani shine ko zai iya kawo karshen rikicin, musamman ma kawar da masu tayar da kayar bayan da suka addabi kasar da ke Yammacin Afirka?

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.