Isa ga babban shafi

'Yan Burkina Faso na bukatar Traore ya rike kasar har lokacin zabe

Yayin da aka bude taron tattauna makomar siyasar kasar Burkina Faso bayan juyin mulkin da sojoji suka yi, yau daruruwan jama’a sun gudanar da zanga zanga inda suke bayyana goyan bayan su na ganin shugaban sojin Kaftin Ibrahim Traore ya zama shugaban gwamnatin rikon kwaryar da zai shirya zabe.

Karo na biyu kenan sojoji na gudanar da juyin mulki a 2022 kadai a kasar da ke Yammacin Afirka
Karo na biyu kenan sojoji na gudanar da juyin mulki a 2022 kadai a kasar da ke Yammacin Afirka © AP/Kilaye Bationo
Talla

Kamfanin dillancin labaran Faransa yace daruruwan mutane ne yau juma’a suka gudanar da zanga zanga a Ouagadougou inda suke bukatar ganin an nada Traore a matsayin shugaban rikon kwarya, duk da yake shugaban sojin ya fito karara yace baya bukatar mukamin.

Sayouba Ouedrapogo, daya daga cikin masu zanga zangar ya shaidawa wakilin kamfanin dillancin labaran cewar Traore kawai suke bukata a matsayin shugaban kasa.

Shi dai Kaftin Traore bai halarci bikin bude taron ba wanda ke da wakilai 300 da suka fito daga jam’iyyun siyasa da shugabannin addinai da kungiyoyin kwadago da kungiyoyin fararen hula tare da wasu daga cikin wakilan mutanen da ‘Yan ta’adda suka raba da muhallinsu.

Kaftin Marcel Medah, daya daha cikin wakilan gwamnatin sojin ne ya karanta sdakon Traore ga mahalarta taron inda ya bukaci zaman lafiya da kuma hadin kan jama’ar kasar.

Traore ya roki jama’ar Burkina Faso da su kawar da banbancin dake tsakaninsu domin bude sabon babi a tafiyar kasar wajen bunkasa harkokin tsaro da zaman lafiya tare da samarwa kasar ci gaba.

Ana saran taron ya amince da shirin mayar da mulki ga fararen hula nan da watan Yulin shekarar 2024.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.