Isa ga babban shafi

Kotun ICC ta kawo karshen shari’ar da ake yi wa wani lauyan kasar Kenya

Kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa (ICC) a jiya Juma’a ta sanar da kawo karshen shari’ar da ake yi wa wani lauyan kasar Kenya da ya rasu, wanda ake zargi da bayar da cin hanci da kuma tsoratarwa a lokacin da kotun ICC ke tuhumar William Ruto,wanda shine shugaban kasar a yanzu.

Lauya Paul Gicheru a zauren kotun hukunta manyan laifuka
Lauya Paul Gicheru a zauren kotun hukunta manyan laifuka © CPI
Talla

An bude shari'ar lauyan mai suna Gicheru a watan Fabrairu a birnin Hague. Masu gabatar da kara sun ce lauyan ya bai wa shaidu cin hanci ta hanyar biyansu kudi har kudin Kenya shilling miliyan daya kwatankwacin Yuro 8,300 tare da yi wa wasu barazana ciki har da daya da yin amfani da makami.

Mista Gicheru dai ya musanta tuhumar da ake masa, inda ya musanta aikata laifin a gaban kotun ICC.

A wata sanarwa da kotun ta ICC ta fitar a ranar Juma’a ta ce ta “kare shari’ar da ake yi wa tsohon lauyan Kenya Paul Gicheru bayan tabbatar da mutuwarsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.