Isa ga babban shafi

Sabon shugaban kasar Kenya William Ruto ya yi rantsuwar kama aiki

Dubban al’ummar Kenya ne suka taru a babban filin wasan birnin Nairobi yau talata a kokarin ganewa idonsu yadda sabon shugaban kasar William Ruto zai karbi rantsuwar kama aiki.

Sabon shugaban kasar Kenya William Ruto.
Sabon shugaban kasar Kenya William Ruto. REUTERS - MONICAH MWANGI
Talla

Da misalin karfe 2 na ranar yau ne William Ruto zai sha rantsuwar kama aikin, bayan gagarumar nasara a zaben ranar 9 ga watan Agusta wanda suka kara tare da madugun adawar kasar Raila Odinga.

Akalla shugabannin kasashe 20 ake sa ran su halarci bikin rantsuwar Ruto a matsayin sabon shugaban kasar Kenya, ciki har da mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo.

Mutane da dama sun jikkata a kokarin shiga filin wasan ta karfin tsiya bayan da jami’an tsaro suka bukaci da su koma gida don kallon bikin rantsuwar ta akwatunan talabijin dinsu.

Tun da sanyin safiyar yau, filin wasan na birnin Nairobi mai daukar mutane dubu 60 ya cika makil yayinda mutane da dama suka samu raunuka a turmutsutsun kokarin shiga filin.

Magoya bayan Ruto baya ga wadanda suka yi tururuwa a cikin filin, wasu dubbai na ci gaba da kotsiya da ababen hawa tare da daga tutar Kenya a manyan titunan kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.