Isa ga babban shafi

Kotun kolin Kenya za ta yi dogaro da wasu batutuwa 9 a shari'ar zaben kasar

Kotun Kolin Kenya ta fitar da wasu batutuwa guda tara da za ta yi dogaro da su wajen yanke hukuncin, karar da ke kalubalantar sakamakon zaben da aka shigar gabanta, zaben da ya bai wa William Ruto nasara.

Zababben shugaban kasar Kenya, William Ruto.
Zababben shugaban kasar Kenya, William Ruto. REUTERS - THOMAS MUKOYA
Talla

Sakamakon zaben ranar 9 ga watan Agusta mai karewa ya bai wa Mataimakin shugaban kasar Uhuru Kenyatta wato William Ruto mai shekaru 55 nasara, abinda kuma tun wancan lokaci abokin hamayyar sa Raila Odinga ya kalubalanci zaben yana mai ayyana shi a matsayin wanda ya cika da almundahana.

Wannan dalili ya sanya Raila Odinga garzayawa Kotu don kalubalantar zaben da bukatar ta soke shi, kasancewar wannan shine karo na biyar da yake tsayawa takarar shugabancin kasar ba tare da samun nasara ba.

Sai dai tuni bayanan farko-farko daga Kotun ke cewa za ta yi kokari wajen fasarra wasu dokoki 9 da Raila Odinga ke bukatar ayi masa fashin baki a kansu, tare da karanto cikakken rahoton bincike game da zargin an yiwa shafin hukumar zaben kasar kutse, da kuma zargin aringizon kuri’a.

Kotun mai alkalai 7 ta kuma yi alakwarin yin karin haske a game da sahalewa amfani da na’urorin zabe da ta yi, wadanda kuma dalilin amfani da su ne ya sanya ta rushe wasu zabubbuka a 2017, abinda ke ciki bautuwan da Odinga ke suka akai.

Kafin ranar yanke hukuncin kuma kotu ta umarci hukumar zaben kasar da ta baiwa Raila Odinga da sauran masu kara damar shiga dukannin nau’o’rorin tattara sakamakon zaben da ta yi amfani da su don su gudanar da binciken su, amma karkashin sanya idanun jami’an hukumar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.