Isa ga babban shafi

Birtaniya ta yi watsi da zargin yin katsalandan a zaben Kenya

Babbar kwamishiniyar da ke wakiltar Birtaniya a Kenya Jane Marriott ta yi watsi da zargin cewa ita da kasar ta sun yi katsalandan a babban zaben kasar da aka kammala cikin watan nan.

Zababben shugaban kasar Kenya, William Ruto.
Zababben shugaban kasar Kenya, William Ruto. AP - Mosa'ab Elshamy
Talla

Mis Marriott na mayar da martani ne kan zargin da aka yi a shafukan sada zumunta a cewa ta matsawa hukumar zabe lamba kan neman ta ayyana William Ruto a matsayin zababben shugaban kasa bayan kammala kada kuri’u a zaben da aka yi ta takaddama a kai tsakanin bangaren gwamnati da ‘yan adawa.

A ‘yan kawanakin nan ne dai, wasu masu amfani da shafukan sada zumunta suka yada hotunan da ba a tantance ba, wadanda ke nuna babbar kwamishiniyar ta Birtaniya Jane Marriott a yayin da take musabaha da zababben shugaba Mista Ruto da kuma shugaban hukumar zaben kasar Kenya mai zaman kanta Wafula Chebukati.

Jim kadan bayan yada hotunan ne kuma, Mis Marriott ta ce ko kadan Birtaniya ba ta goyon bayan kowane dan takara ko kuma jam’iyyun da suka fafata a zaben shugabancin kasar ta Kenya ba, tare da bayyana zargin a matsayin maras tushe.

Marriott ta ce Kenya za ta ci gaba da kasancewa muhimmiyar abokiyar huldar Birtaniya, kuma a shirye suke da su tallafa wa shugabannin da jama'a suka zaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.