Isa ga babban shafi

Kotun kolin Kenya ta tabbatar da Ruto ne ya lashe zaben shugabancin kasar

Kotun kolin Kenya ta yi watsi da karar da Raila Odinga ya shigar a gabanta, yana kalubalantar sakamakon zaben shugabancin kasar da aka gudanar, inda aka bayyana William Ruto a matsayin wanda ya yi nasara.

Zababben shugaban kasar Kenay aWilliam Ruto kenan, lokacin da ya karbi takardar shaidar lashe zabe daga hukumar zaben kasar
Zababben shugaban kasar Kenay aWilliam Ruto kenan, lokacin da ya karbi takardar shaidar lashe zabe daga hukumar zaben kasar REUTERS - THOMAS MUKOYA
Talla

Dama dai  William Ruto ya bayyana cewar a shirye yake ya amince da duk hukuncin da kotun kolin kasar ta yanke a wannan Litinin.

Hukumar zaben kasar mai zaman kanta IEBC ta bayyana Ruto a matsayin wanda ya lashe zaben da sama da kashi 50 na kuri’un da aka kada, yayin da abokin karawar tasa Raila Odinga da ke samun goyon bayan shugaban kasar ya samu kashi 48.65.

Odinga ya kalubalanci wannan sakamakon zaben a gaban kotu bisa zargin babakeren da ya ce an yi a yayin kidayar kuri’un.

"Wannan shawara ce baki daya da ke cewa an yi watsi da korafe-korafen da aka shigar gaban kotu, saboda haka aka ayyana wanda ake kara na farko wato William Ruto a matsayin zababben shugaban kasa,” in ji babbar mai shari’a Martha Koome.

Mataimakin shugaban kasar Ruto, mai shekaru 55, ya tsallake rijiya da baya da tazarar kasa da kashi biyu cikin dari a fafatawar da suka yi da Odinga, wani gogaggen dan siyasar adawa da yanzu haka ke samun goyon bayan jam'iyya mai mulki.

Odinga ya ci gaba da cewa an yi kutse a rumbun tattara bayanan hukumar zaben mai zaman kanta kuma aka shigar da wasu bayanan sakamako na bogi, sannan kuma akwai kuri’u sama da dubu 140 da ba a sanya su cikin wadanda aka kidaya ba.

Ko da yake an gudanar da zaben cikin lumana, amma sakamakon ya haifar da zanga-zangar nuna bacin rai a yankunan da Odinga ke da magoya baya, lamarin da ya sa ake fargabar cewa sakamakon da ake ta cece-kuce da shi zai iya haifar da tashin hankali a kasar da ke da tarihin tashe tashen hankula bayan zaben.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.