Isa ga babban shafi

William Ruto ya lashe zaben shugabancin kasar Kenya

Mataimakin shugaban kasar Kenya, William Ruto ya lashe zaben shugabancin kasar, inda ya kayar da abokin burmin sa Raila Odinga wanda ke samun goyon bayan shugaban kasar Uhuru Kenyatta.

Mataimakin shugaban Kenya kenan William Ruto wanda ya lashe zaben shugabancin kasar
Mataimakin shugaban Kenya kenan William Ruto wanda ya lashe zaben shugabancin kasar AFP - SIMON MAINA
Talla

Shugaban hukumar zaben kasar Kenya a ranar Litinin ya ayyana mataimakin shugaban kasar William Ruto a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar, duk da cewa wasu kwamishinonin sun ki amincewa da sakamakon zaben.

Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta Wafula Chebukati ya ce Ruto ya lashe zabe da kusan kuri'u miliyan 7.18 (kashi 50.49) yayin da abokin hamayyarsa Raila Odinga ya samu kuri'u miliyan 6.94 (kashi 48.85).

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.