Isa ga babban shafi

Zaben Kenya: Raila Odinga da William Ruto na tafiya kan-kan-kan a yawan kuri'u

Zuwa yanzu hukumar zaben Kenya ta tattara akalla kashi 90 na kuri'un da al’ummar Kenya su ka kada a zaben shugaban kasa na jiya Talata, zaben da ya gudana ba tare da tashin hankali ba duk da hasashen yiwuwar fuskantar rikicin, ko da ya ke ba a fito zaben kamar yadda ya kamata ba a wasu sassan kasar.

Manyan 'yan takarar neman kujerar shugabancin kasa a Kenya.
Manyan 'yan takarar neman kujerar shugabancin kasa a Kenya. © REUTERS / BAZ RATNER
Talla

Duk da ya ke zai dauki kwanaki gabanin iya fitar da sakamakon zabe, amma bayanai na nuna yadda ake tafiya kan-kan-kan tsakanin manyan 'yan takarar kasar biyu wato tsohon Firaminista Raila Odinga da kuma mataimakin shugaban kasa William Ruto .

A jawabin da ya gabatar cikin daren Talata, shugagabn hukumar zaben kasar, Wafula Chebukati ya yi kira ga al’ummar Kenya su kasance masu hakuri a yayin da hukumarsa ke aikin kirga kuri’u.

Da dama na zaman dar dar a yayinda su ke dakon sakamakon zaben, ganin cewa tun daga shekarar 2002 babu wani zaben da ba a samun takaddama a kan sakamako ba.

Ko a shekarar 2007, rikicin siyasa mai nasaba da kabilanci ne ya biyo bayan zaben, inda sama da mutane dubu 1 suka mutu, a yayin da a shekarar 2017 da Odinga kalubalanci sakamakon zaben, hukumomi suka cinna wa masu zanga-zanga jami’an tsaro, lamarin da ya yi sanadin mutuwar gwammai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.