Isa ga babban shafi

'Yan takara 4 da ke fafatawa a zaben shugaban kasar Kenya

'Yan takara 4 ne ke fafatawa domin samun nasarar zama shugaban kasar Kenya, a dai dai lokacin da ake fama da fargabar tashin hankali, sakamakon yadda ake yada labaran karya ta kafofin sada zumunta da kuma barazanar barkewar rikicin kabilanci.

Wata rumfar zabe a Kenya.
Wata rumfar zabe a Kenya. © RFI/Laura-Angela Bagnetto
Talla

'Yan takarar neman kujerar shugabancin kasar sun hada da mataimakin shugaban kasa William Ruto da shugaban 'yan adawa Raila Odinga da kuma David Mwaure Waihiga baya ga Farfesa George Wajackoyah.

A shekarar 2007, mutane sama da 1,100 suka rasa rayukan su sakamakon tashin hankalin da ya biyo bayan zaben da aka fafata tsakanin shugaba Mwai Kibaki na wancan lokaci da Raila Odinga, wanda ya yi ikrarin lashe zaben.

Sakamakon rikicin kungiyar kasashen Afirka ta shiga tsakani wajen sasanta bangarorin guda biyu, abinda ya kaiga kafa gwamnatin rikon kwarya tsakanin shugaban Mwai Kibaki, wanda ya ci gaba da zama a kujerar sa da Raila Odinga, wanda ya zama Firaminista, yayin da shugaba mai ci Uhuru Kenyatta ya zama mataimakin Firaminista.

Bayan kamala wa’adin Kibaki, Kenyatta ya maye gurbin sa inda ya ke shirin kammala wa’adin sa, yayin da ya ke goyawa tsohon maigidana sa Odinga baya, sabanin mataimakin sa William Ruto wanda basa ga maciji da juna.

Yanzu haka dai ana fargabar samun rikici dangane da zaben saboda yadda kabilanci ya yi tasiri a siyasar Kenya abinda ya kaiga wasu tserewa daga garuruwan su zuwa kasashen da ke makota domin kare rayukan su.

Kasar Amurka ta yi gargadi da 'yan kasar ta da su kaucewa zuwa wasu yankunan Kenya saboda irin wannan fargaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.