Isa ga babban shafi

Odinga ya kaurace wa zaman muhawarar siyasa a Kenya

Dan takarar shugabancin kasa a Kenya Raila Odinga ya kaurace wa zaman muhawarar da aka shirya gudanarwa gabanin babban zaben kasar na ranar 9 ga watan Agusta mai zuwa, inda aka ga fuskar William Ruto kadai a zauren muhawarar.

Raila Odinga
Raila Odinga AFP - SIMON MAINA
Talla

Bayan da kwamitin yakin neman zaben Raila Odinga mai shekaru 77 ya sanar da janyewa daga muhawarar a Lahadin da ta gabata ne masu shiryawa suka zabi tafiyar da muhawarar ta jiya Talata kamar yadda aka tsara amma da dan takara guda.

Yayin zaman muhawarar ta jiya Talata da aka ga fuskar Ruto mai shekaru 55 shi kadai a zauren, ya amsa tambayoyi daga ‘yan jarida biyu, duk da cewa muhawarar ba ta yi armashi kamar yadda aka tsara ba.

Odinga wanda ya sha alwashin halartar wani taron jin ra’ayoyin jama’a da ake shirin gudanarwa a gabashin birnin Nairobi wanda kuma za a haska kai tsaye ta gidajen talabijin don amsa tambayoyi daga al’ummar kasar.

Cikin sanarwar da kwamitin yakin neman zaben Odinga ya fitar, kakakinsa ya ce, William Ruto ya ki amincewa a tattauna batutuwa masu alaka da rashawa wanda ya sanya Odinga kauracewa zaman.

Tun farko Ruto ya mika bukatar ganin zaman muhawarar bai tabo batutuwa masu alaka da Rashawa ko kyakkyawan shugabanci ko kuma da’a da cancanta ba, wanda kuma masu shirya muhawarar suka amince lamarin da baiyiwa Odinga dadi ba.

A cewar Raila Odinga kaucewa baututuwan da Ruto ya bukata tamkar cin mutunci ne ga al’ummnar Kenya, wadanda ke fatan samun ingantaccen shugaban da zai ciyar da kasar gaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.