Isa ga babban shafi

'Yan takarar shugaban kasa sun kammala yakin neman zabe a Kenya

An kammala yakin neman zaben shugaban kasar Kenya, wanda ake shirin gudanarwa gobe Talata, sai dai rahotanni na nuna cewar ana ci gaba da fuskantar matsalar yada labaran karya da magoya bayan jam’iyyun kasar keyi ta kafofin sada zumunta da zummar bata yan takarar adawa.

Manyan 'yan takarar shugaban kasa a Kenya Raila Odinga tare da William Ruto.
Manyan 'yan takarar shugaban kasa a Kenya Raila Odinga tare da William Ruto. REUTERS - BAZ RATNER
Talla

Magoya bayan 'yan takarar da ke sahun gaba wajen takarar zaben shugaban kasar da za a yi gobe da suka hada da mataimakin shugaban kasa William Ruto, wanda ya zama shugaban 'yan adawa da tsohon dan siyasa Raila Odinga, wanda ya dade ya na takara ba tare da samun nasara ba, na yada labaran cewar kowanne bangare na yunkurin shirya magudi.

Benedict Manzin, na cibiyar asirin Birtaniya da ake kira Sibylline ya ce suna ci gaba da ganin bayanan karya da ake yadawa a kafofin sada zumunta, wadanda ke kokarin bata yan takarar da kuma yin illa akan sakamakon zaben da za’a gabatar.

A shekarar 2007, kasar Kenya ta fada rikicin siyasa da kabilanci, sakamakon tashin hankalin da ya biyo bayan zaben shugaban kasar da akayi, wanda kotun koli ta soke saboda tafka magudin da akayi, abinda ya kaiga kafa gwamnatin hadin kai tsakanin tsohon shugaban kasa Mwai Kibaki da Raila Odinga.

Rikicin da ya biyo bayan wancan zaben yayi sanadiyar mutuwar mutane sama da 1,100, abinda ke sanya jama’a fargaba duk lokacin da Kenya zata sake gudanar da zabe.

Kungiyoyin fararen hula da hukumar dake sanya ido a kafofin sada zumunta sun yi gargadin dangane da irin wadannan labaran karya wadanda ke barazanar tada hankalin jama‘a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.