Isa ga babban shafi

Hukumar zaben Kenya ta ce akwai matattu cikin kudin masu zabe

Hukumar zaben Kenya ta ce a ci gaba da tantace rijistar masu kada kuri’a da take yi, ta gano kusan mutane dubu dari biyu da 50 da suka mutu kuma sunayensu na cikin rijistar ta.

Wafula Chebukati,Shugaban hukumar zaben Kenya
Wafula Chebukati,Shugaban hukumar zaben Kenya REUTERS/Thomas Mukoya
Talla

Hukumar zaben kasar ta Kenya ta ce akwai wasu kusan rabin miliyan da suka yi rijista fiye da sau daya, sai kuma wasu dubu dari biyu da 60 da sukayi rijsta ba tare da cikakkun bayanan su ba.

Ranar 9 ga watana Agusta ne za a gudanar da zaben yan majalisu  da na Shugaban kasa,inda rahotanni suka bayyana cewa a duk lokacin da aka gudanar da zabe ana fuskantar tashin hankali.

Zaben kasar Kenya na wannan shekara,hukumar zaben kasar ta dau matakan da suka dace na kaucewa fadawa cikin rudani,jami'an ta na ci gaba da gudanar da ayukan da suka dace don tattance yan kasar daya bayan daya da doka ta baiwa dama na suka kada kuri'a.

Shugaban hukumar Wafula Chebukati ya ce aikin tantancewar da suke yi zai haifar da tsaiko wajen wallafa sunayen wadanda sukayi rijistar zabe ganin yadda samada mutane miliyan guda abin ya shafa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.