An yi wa tsohon shugaban Kenya Moi Kibaki jana'izar karramawa
A yau aka gudanar da jana'izar tsohon shugaban kasar Kenya Mwai Kibaki, wanda ya rasu mako guda da ya wuce yana da shekaru 90 a duniya.
Wallafawa ranar:
Mista Kibaki shi ne shugaban kasa na uku a tarihin kasar ta Kenya, wanda ya fara mulki daga watan Disambar 2002 zuwa Afrilun 2013, bayan da ya gaji gwamnatin mulkin kama-karya ta Daniel Arap Moi.
Moi shi ne shugaban da ya gabaci shugaban Kenya mai ci, Uhuru Kenyatta, wanda shine dan farko ga shugaban Kenya na farko, Jomo Kenyatta.
A safiyar Juma’ar nan , aka ayyana hutu a kasar, don gudanar da jana’izar tsohon shugaban da aka yi a filin wasannin motsa jiki na Nyayo da ke tsakiyar babban birnin kasar Nairobi, yayin da ya samu rakiyar ayarin sojoji da tarin al’uma, bayan da aka fito da shi daga fadar shugaban kasar.
Baya ga jami’an gwamnati, an samu tarin jami'ai, jakadu, da shugabannin kasashe da dama da suka halarci taron, ciki har da shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa da na Sudan ta Kudu Salva Kiir.
Mwai Kibaki, tsohon farfesa ne a fannin tattalin arziki da ya samu horo a Uganda da Landan, an kuma zabe shi ne a shekara ta 2002 bisa alkawarin yaki da cin hanci da rashawa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu