Isa ga babban shafi

Tsohon Shugaban Kenya Mwai Kibaki ya mutu

tsohon Shugaban kasar Kenya Mwai Kibaki shugaban kasar na uku da ya shugabancin kasar tsawon shekaru 10 a wani lokaci da kasar ta yi fama da rigigimun siyasa tun bayan samun inci kai ya rasu ya na mai shekaru 90 a Duniya.

Mwai Kibaki tsohon shugaban kasar Kenya
Mwai Kibaki tsohon shugaban kasar Kenya (Photo : Reuters)
Talla

Da samun labarin rasuwar tsohon Shugaban kasar,Uhuru Kenyatta shugaban kasar mai ci ,ya bayyana alhinin sa tareda danganta mammacin a matsayin mutum mai hangen nisa tareda sanin abinda ya kamata a fagen tafiyar da jama'a.

Tsohon Shugaban kasar Kenya Mwai Kibaki
Tsohon Shugaban kasar Kenya Mwai Kibaki © AFP/Tony KARUMBA

Mwai Kibaki,tsohon farfesa a fanin tattalin arziki,ya samu wannan horo ne a kasar Uganda kafin daga bisali ya isa Ladan dake Birtaniya don samun kwarewa a fanin tattalin arziki.

Ya na daga cikin mutanen da suka taka muhimiyar rawa a fagen siyasar kasar ta Kenya tun bayan samun inci kai a shekara ta 1963.

Shugaban kasar kenya Mwai Kibaki tare da  Prime Minista Raila Odinga
Shugaban kasar kenya Mwai Kibaki tare da Prime Minista Raila Odinga Reuters/Noor Khamis

Ya dahe kujerar shugabancin kasar Kenya a shekara ta 2002 tareda daukar alkawalin yakar cin hanci da rashawa,bayan da Shugaba Daniel Arap Moi ya shugabancin Kenya tsawon shekaru 20.

Marigayi tsohon Shugaban kasar Kenya dan kabilar Kikuyu na daga cikin mutanen da suka taimakawa shugaba Uhuru Kenyatta na shata manufofin siyasa zuwa shekara ta 2030 a kasar ta Kenya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.