Kenya ta kori shugaban kamfanin makamashi na Rubis mallakin Faransa
Kasar Kenya ta kori shugaban kamfanin makamashi na Rubis mallakin Faransa biyo bayan ta’azzarar matsalar karancin man fetur, lamarin da ya tilasta wa jama’a yin dogon layi a gidajen sayar da man.
Wallafawa ranar:
Ma’aikatar makamashi ta Kenya ta ce, an kori Jean-Christian Bergeron ne sakamakon zargin sa da yi wa tattalin arzikin Kenya zagon-kasa ta hanyar boye man fetur da kuma fitar da shi zuwa can ketare a daidai lokacin da kasar ke cikin bukata.
Ta bakin Ministan cikin gidan kasar ta Kenya Monica Juma yayin ganawa da manema labarai,jami'in ya fice daga kasar ta Kenya,hukumomi cikin gaggawa zasu magance wannan matsala.
Kamfanin na Rubis ya musanta zargin da ake masa na kara kudin man a kasar ta Kenya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu