Isa ga babban shafi
kenya - tsaro

Kenya ta tsaurara matakan tsaro saboda fargabar yiwuwar kai hare-hare

Kasar Kenya ta tsaurara matakan tsaro a babban birnin kasar, Nairobi da wasu biranen kasar bayan da wasu kasashen Turai suka yi gargadin yiwuwar kai hare-hare.

Daya daga cikin 'Yan sandan Kenya dake sintiri a titunan babban birnin kasar Nairobi 7/05/2020.
Daya daga cikin 'Yan sandan Kenya dake sintiri a titunan babban birnin kasar Nairobi 7/05/2020. REUTERS/Thomas Mukoya
Talla

An ga jami’an ‘yan sanda dauke da manyan makamai na ta sintiri a titunan birnin Nairobi ranar Juma’a, yayin da aka tsaurara tsaro a ofisoshin gwamnati da gine-ginen jama’a da kuma manyan kantuna.

Ofishin jakadancin Faransa a Kenya ya fitar da wata sanarwa inda acinta ya gargadi 'yan kasarsa kan "hadarin kai hari a Nairobi cikin kwanaki masu zuwa" a yana mai ba da shawarar "kaurace wa wuraren da 'yan kasashen waje ke zuwa" kamar otal-otal, gidajen cin abinci da manyan shaguna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.