Isa ga babban shafi
Kenya

Dan sandan Kenya ya harbe mutane 6 tare da kashe kansa

Wani jami’in dan sandan kasar Kenya ya harbe mutane shida har lahira, ciki har da matarsa, tare da jikkata wasu biyu kafin daga bisani ya harbe kansa da bindiga.

Wasu 'yan sandan kasar Kenya yayin kokarin dakile wata zanga-zanga a birnin Nairobi cikin shekarar 2014.
Wasu 'yan sandan kasar Kenya yayin kokarin dakile wata zanga-zanga a birnin Nairobi cikin shekarar 2014. AFP/Simon Maina
Talla

Tuni dai lamarin ya haifar da zanga-zangar da fusatattun mazauna yankin marasa galihu a birnin Nairobi suka rufe hanya da kona tayoyi.

Binciken ‘yan sanda ya gano cewar, jami’in nasu y afara harbin matarsa a wuya da bindiga kirar AK-47, kafin ya budewa sauran jama’ar dake kusa wuta, nan take kuma ya kashe mutane 6 kafin ya kashe kansa.

A bangaren wadanda suka jikkata kuma, an kwantar da wasu mutane biyu a asibiti.

Har yanzu dai ba a tantance dalilin ya sanya dan sandan Kenyan tafka wannan ta’asa ba, said ai wata majiya ta ce jami’in da matarsa sun dade suna samun rashin fahimtar juna.

Wannnan dai ba shi ne karo na farko da ake samon jami’an tsaro a Kenya suna halaka abokan zamansu ba.

A watan da ya gabata, wani jami'in dan sanda ya bude wuta kan abokan aikinsa a tsakiyar kasar Kenya, inda ya harbe daya a kai kafin ya gudu.

A watan Maris kuwa, wani jami’in ‘yan sanda ya kashe daya daga cikin manyan jami’ansa a yammacin Kenya, bayan wata takaddama kan tura su zuwa aiki, sannan kuma ya kashe kansa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.