Isa ga babban shafi
KENYA-TSARO

Kenyatta ya kori shugaban gidajen yari saboda tserewar 'yan ta'adda

Gwamnatin Kenya ta kori shugaban gidajen yarin kasar Wycliffe Ogallo sakamakon abinda kunyar da tace ya auku, lokacin da wasu mutane 3 da ake zargi da harin ta’addanci suka gudu daga gidan yarin da ake tsare da su a cikin wannan makon.

Shugaban Kenya Uhuru Kenyatta
Shugaban Kenya Uhuru Kenyatta YVES HERMAN POOL/AFP/File
Talla

Shugaban hukumar binciken kasar yace an kuma kama tubabben shugaban kula da gidajen yarin na kasa Ogallo tare da jami’in kula da gidan yarin da mutanen suka gudu tare da mataimakin sa.

Ministan cikin gidan kasar Fred Matiangi ya bayyana tserewar mutanen a matsayin rashin hankali da kuma abin kunya ga kasa, yayin da ya sanar da kama jami’an dake gadin gidan yarin su 7 lokacin da lamarin ya auku.

Ministan ya kuma bayyana sanya ladar Dala 535,000 ga duk wanda zai bada rahotan inda za’a kama wadanda suka gudun da zummar ganin an yi musu shari’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.